Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaINEC na nazarin hukuncin Kotun Ƙoli kan cancantar wasu ’yan takara

INEC na nazarin hukuncin Kotun Ƙoli kan cancantar wasu ’yan takara

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, na duba matakin da za ta ɗauka kan wasu ’yan takara da ake zargin zaɓukan fidda gwamni da suka fito sun saɓa wa tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.

Rahoton Daily Trust ya ce INEC na jiran samun kwafin hukuncin Kotun Ƙoli da aka tabbatar da sahihancinsa (CTC), kafin sashen shari’a na hukumar ya nazarci hukuncin tare da gabatar da shawarwari ga kwamishinonin hukumar.

Kwamishinan INEC mai kula da yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya tabbatar da cewa hukumar za ta nazarci hukuncin bayan ta samu kwafin.

Ya ce akwai wasu batutuwa da ke buƙatar ƙarin bayani, musamman game da makomar ’yan takarar da hukuncin zai iya shafa.

Rahoton ya ce batun ya shafi tanade-tanaden Sashe na 77 na Dokar Zaɓe, wanda ya tanadi cewa jam’iyyu su gabatar da ingantacciyar rajistar mambobinsu ga INEC kafin gudanar da zaɓen fidda gwani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments