Gwamnatin Jihar Kano ta fara rabon murhun girki mara hayaƙi guda 3,400 da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta bai wa mata masu ƙaramin ƙarfi a jihar.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Dahir Hashim, ne ya ƙaddamar da rabon murhun a ranar Lahadi a Kano. Ya ce shirin na da nufin rage haɗarin da amfani da itacen girki ke haifarwa ga lafiyar jama’a da muhalli.
Dr. Hashim ya bayyana cewa zuwa yanzu an riga an raba murhun girki 800 ga mata masu ƙaramin ƙarfi a sassa daban-daban na jihar.
“Waɗannan murhun girki marasa hayaƙi na cikin guda 3,400 da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta ware wa Kano,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tallafa wa kowace daga cikin mata 800 da aka fara rabawa murhun da N25,000 domin ƙarfafa sana’o’insu da inganta hanyoyin samun abin dogaro da kai.
A cewar kwamishinan, shirin ya yi daidai da manufar gwamnatin jihar ta rage fitar da hayaki mai gurɓata muhalli tare da ƙarfafa amfani da hanyoyin girki masu tsafta maimakon hanyoyin gargajiya.
Dr. Dahir Hashim ya ce mata sun shafe shekaru suna fuskantar barazanar lafiya sakamakon shakar hayaƙin da itacen girki ke haifarwa, musamman saboda yawan amfani da murhun gargajiya.
Ya bayyana cewa yawan shakar irin wannan hayaƙi na iya jawo munanan matsalolin lafiya, musamman cututtukan numfashi, yana mai kwatanta illar da shakar hayaƙin da ake samu daga shan fakitin sigari da dama a kullum.
Kwamishinan ya ce shirin murhun girki marasa hayaƙin na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin yaƙi da sauyin yanayi tare da inganta lafiya da rayuwar mata masu ƙaramin ƙarfi a jihar.
Ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa samar da murhunan, sannan ya bukaci waɗanda suka amfana da su da su yi amfani da su yadda ya kamata.
Dr. Hashim ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin faɗaɗa shirye-shiryenta na amfani da makamashi mai tsafta, ciki har da sanya fitilun tituna da wasu Ma’aikatu, Hukumomi da Sassan Gwamnati (MDAs) su riƙa amfani da hasken rana.