Wani sabon bincike ya alakanta wasu manyan jami’an gwamnati na yanzu da na baya 61 na Najeriya da kadarori 284 a Amurka, waɗanda darajarsu ta kai kusan dala miliyan 271, wato kimanin naira biliyan 370.
Binciken da PPLAAF tare da Anti-Corruption Data Collective suka gudanar ya ce kadarorin an saye su ne tun daga shekarar 1991, ciki har da kadarori 152 da aka saya lokacin da jami’an ke kan mukaman gwamnati.
Rahoton mai taken Dirty Deeds: How Top Nigerian Officials Bought a Piece of America ya ce 39 daga cikin jami’an da aka bincika an taɓa zarginsu, gurfanar da su ko yanke musu hukunci kan zargin cin hanci da rashawa.
Binciken ya kuma gano cewa kadarori 230, waɗanda darajarsu ta kai kusan dala miliyan 232, an saya su ba tare da wata bayyananniyar hanyar samun kuɗin sayen ba, kamar jinginar banki.
Sai dai PPLAAF ta jaddada cewa binciken bai tabbatar da cewa an sayi dukkan kadarorin da kuɗaɗen da aka sace ba, inda ta buƙaci hukumomin Najeriya da Amurka su binciki tushen kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin.