Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garin Kagara da ke ƙaramar hukumar Goronyo a Jihar Sokoto, inda aka samu asarar rayukan mutane uku, ciki har da wani mutum mai fama da matsalar tabin hankali.
Lamarin ya faru ne a daren Asabar, lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye garin tare da kai farmaki ga mazauna yankin.
Bayan kashe mutanen uku, maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane 28, inda suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
Harin ya haifar da fargaba da damuwa a tsakanin mazauna Kagara da kewaye, yayin da ake ci gaba da kokarin gano inda mutanen da aka yi garkuwa da su suke da kuma ganin an kubutar da su.
Rahotanni sun ce har zuwa yanzu, ba a samu cikakken bayani kan halin da mutanen da aka sace suke ciki ba.