Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiEl-Rufai: Kungiyar Musulmi ta musanta goyon bayan kalaman Christopher Musa

El-Rufai: Kungiyar Musulmi ta musanta goyon bayan kalaman Christopher Musa

Ƙungiyar Southern Kaduna Muslim Ummah Development Association (SOKAMUDA) ta nesanta kanta da wani rahoto da ya bayyana cewa ta goyi bayan Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, kan kalaman da ya yi a baya-bayan nan game da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

SOKAMUDA ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Sakataren ƙungiyar, Alhaji Ahmad Mairiga Yandeh, ya sanya wa hannu ranar Litinin.

Ƙungiyar ta ce ba a tuntube ta ba, kuma ba ta wakilci kanta a cikin matsayin da aka danganta ga wata ƙungiyar Musulmi da Kirista da ta ce tana goyon bayan Ministan Tsaron.

SOKAMUDA ta mayar da martani ne ga wani rahoto da aka wallafa a intanet mai taken: “El-Rufai: Ƙungiyar Musulmi da Kirista ta goyi bayan Ministan Tsaro Musa.”

Ƙungiyar ta ce taken rahoton ya haifar da tunanin cewa matsayin da aka bayyana ya wakilci Musulmi baki ɗaya, Musulman Jihar Kaduna ko kuma al’ummar Musulmin Kudancin Kaduna.

Sai dai ƙungiyar ta ce tana mutunta Janar Musa a matsayin “ɗan Kudancin Kaduna mai daraja kuma babban jami’in sojan Najeriya.”

Ta ƙara da cewa girmama mutum ba yana nufin amincewa da duk wata magana ko matakin da aka danganta masa ba tare da tambaya ba.

SOKAMUDA ta ce matakin da ta ɗauka ya samo asali ne daga ƙudurin da take da shi na tabbatar da zaman lafiya, mutunta juna, shugabanci nagari da kuma kyakkyawar alaƙa tsakanin al’ummomi daban-daban a Jihar Kaduna

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments