Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaMiyetti Allah ta gindaya wa Tinubu sharaɗin samun goyon bayanta a 2027

Miyetti Allah ta gindaya wa Tinubu sharaɗin samun goyon bayanta a 2027

Ƙungiyar Miyetti Allah ta bayyana cewa za ta goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027 ne kawai idan an saki shugaban ƙungiyar na ƙasa, Bello Bodejo, da ke hannun Hukumar DSS.

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah a Jihar Nasarawa, Akhajo Abubakar, ya bayyana matsayar ƙungiyar ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan Bello Bodejo da ke Uke, a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Abubakar ya ce ƙungiyar ba za ta ɗaure kanta da wata jam’iyya ba, sai dai za ta duba ‘yan siyasar da suka nuna damuwa da muradun al’ummar Fulani da kuma shirye-shiryen inganta rayuwarsu.

Ya ce: “Ba mu zaɓi APC ba domin ta kama shugabanninmu. A wannan karon, ƙuri’unmu za su tafi ne ga waɗanda suke son ci gabanmu.”

A cewar shugaban ƙungiyar a Nasarawa, al’ummar Fulani na da sama da masu zaɓe miliyan ɗaya a jihar, sai dai bai gabatar da wata hujja ko bayanan da suka tabbatar da wannan adadi ba.

Ƙungiyar ta ce matsayinta kan zaɓen 2027 zai dogara ne kan yadda ‘yan siyasa za su nuna kishin ci gaban al’ummar Fulani, da kuma yadda za su mutunta muradun ƙungiyar.

Wannan matsaya ta zo ne yayin da jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin al’umma ke ƙara bayyana matsayinsu gabanin zaɓen 2027.

Bello Bodejo dai na fuskantar shari’a, yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan tsare shi da kuma batun bel ɗinsa.

A halin yanzu, ba a bayyana ko gwamnatin tarayya ko jam’iyyar APC ta mayar da martani kai tsaye kan wannan matsaya ta Miyetti Allah ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments