Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiIna samun miliyan 10 a duk wata a lokacin da nake sana’ar...

Ina samun miliyan 10 a duk wata a lokacin da nake sana’ar ƙosai – Gwamnan Akwa Ibom

Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana cewa kafin ya shiga harkokin siyasa, ya taɓa samun kuɗin shiga da ya kai sama da Naira miliyan 10 a duk wata daga sana’ar sayar da ƙosai da biredi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron addu’ar wata-wata na jihar, inda kalaman nasa suka fara jan hankali a kafafen yaɗa labarai a ranar Laraba.

A cewarsa, ya fara sana’ar ne ta hanyar sayar da ƙosai da biredi, inda ya ƙirƙiri abin da ya kira “Akara Burger” wato buɗe biredi a saka ƙosai a ciki domin sayarwa ga ma’aikatan kamfanoni da sauran kwastomomi.

Ya ce ma’aikatan kamfanoni kan tsaya da safe domin sayen abincin tare da shan shayi, kafin daga bisani ya faɗaɗa sana’ar ya buɗe shagon kofi.

Gwamnan ya ce:

“Har yanzu muna da wannan shago. A can na fara sayar da ƙosai da biredi.

A wancan lokacin, ina kiransa ‘Akara Burger’, inda muke buɗe biredi mu saka ƙosan a ciki.

Ma’aikatan da ke zuwa kamfanoni suna tsayawa da safe su saya, tare da shan shayi. Daga baya muka buɗe shagon kofi.”

Ya ƙara da cewa sana’ar ta kasance babbar hanyar samun kuɗin shiga a gare shi, inda a cewarsa, a wasu lokuta kuɗin da yake samu daga sana’ar ya kai Naira miliyan 10 ko fiye a wata.

Gwamna Eno ya bayyana labarin ne a matsayin misali na yadda sana’o’in ƙanana za su iya bunƙasa su zama manyan harkokin kasuwanci idan aka samu jajircewa da kyakkyawan tsari.

Bayanin gwamnan ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman kan yadda sana’ar ƙosai da biredi za ta iya samar da irin wannan adadi na kuɗin shiga a wata.

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa sana’ar tasa ba ta tsaya kan sayar da ƙosai kawai ba, domin ta haɗa da biredi, shayi da kuma shagon kofi, tare da samun kwastomomi daga ma’aikatan kamfanoni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments