Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sake duba tsarin rancen kuɗin karatu na NELFUND tare da yiwuwar yafe wasu basussukan ɗalibai.
Atiku, ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke bayyana NELFUND a matsayin hanyar da ta sauƙaƙa ilimi, yana mai cewa rance ba zai iya zama madadin tallafin karatu ba.
Shaibu ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙara tsadar karatu a wasu makarantu, sannan ta koma tana bai wa ɗalibai rance domin su iya biyan kuɗaɗen karatu. Ya ce wannan ba cikakkiyar mafita ba ce, domin ɗalibai za su kammala karatu da basussuka.
A cewarsa, shirin Atiku zai mayar da hankali wajen rage tushen tsadar ilimi, sannan a duba yiwuwar yafewa ɗaliban da suka cancanta bashin karatun da suka ci.
Ya kuma ƙalubalanci fadar shugaban ƙasa da ta bayyana yadda rage farashin makamashi da man fetur da Atiku ke cewa zai shafi NELFUND ko albashin ma’aikata. Shaibu ya ce rage kuɗin makamashi da sufuri zai taimaka wajen ƙara ƙarfin kuɗin shiga na ma’aikata da kuma rage nauyin da ke kan ɗalibai.