Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce ta dakile wani yunƙurin bore da wasu sojoji suka yi a Yamai, babban birnin ƙasar, bayan da aka shafe tsawon dare ana jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a wasu sassan birnin.
Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:20 na dare, lokacin da wasu sojoji suka kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.
Sai dai ministan ya ce sauran dakarun ƙasar sun mayar da martani cikin gaggawa tare da dakile yunƙurin, inda daga bisani aka maido da zaman lafiya da tsaro.
Rahotannin farko sun ce an ji harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman Yamai, fadar shugaban ƙasa da wasu sansanonin soji.
Wasu majiyoyin tsaro sun kuma bayyana cewa an yi yunƙurin kutsawa wasu muhimman wurare, yayin da wasu daga cikin waɗanda ake zargi suka tsere.
Gwamnatin Nijar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Har yanzu dai hukumomi ba su bayyana ko akwai waɗanda suka mutu ko suka jikkata sakamakon lamarin ba.