Gwamnatin Najeriya ta ce kasar ta samu karin kudaden shiga da suka kai Naira tiriliyan 15.8 cikin watanni 30, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauyen da aka yi a tsarin canjin kudaden kasashen waje.
A cewar gwamnatin, karin kudaden ya samu ne tsakanin Yunin 2023 da Disamban 2025, bayan aiwatar da wasu daga cikin manyan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnatin ta bayyana cewa daya daga cikin muhimman abubuwan da suka taimaka wajen samun karin kudaden shi ne cire tallafin man fetur, wanda ya sauya tsarin kashe kudaden gwamnati da kuma yadda ake rabon kudaden shiga.
Haka kuma, sauye-sauyen da aka yi a tsarin kasuwar canjin kudaden waje, wato FX, sun taimaka wajen kara kudaden da ake samu a asusun gwamnati.
A cewar gwamnatin, jihohi da kananan hukumomi ne suka fi cin gajiyar karin kudaden, saboda karuwar kudaden da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati ta hanyar Asusun Tarayya.
Gwamnatin ta ce wadannan sauye-sauye na daga cikin matakan da take ganin za su taimaka wajen kara kudaden shiga da kuma inganta tsarin tattalin arzikin Najeriya.