Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSanata Barau ya wakilci Tinubu a taron kasa da kasa kan tsaro...

Sanata Barau ya wakilci Tinubu a taron kasa da kasa kan tsaro a Abuja

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wani babban taron ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Abuja, wanda ya mayar da hankali kan tsaron ƙasa da bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa.

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League) ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS).

Taron ya samu halartar manyan malaman addini, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki daga Najeriya da wasu ƙasashen duniya.

Da yake gabatar da saƙon Shugaba Tinubu a madadinsa, Sanata Barau ya ce taron ya zo ne a lokacin da duniya ke fuskantar sabbin ƙalubale da barazanar tsaro da ke buƙatar kulawar ƙasashe da hukumomi.

Ya buƙaci mahalarta taron da su yi nazari mai zurfi kan matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya da nahiyar Afrika, tare da samar da shawarwari da za su iya taimakawa wajen samun mafita mai ɗorewa.

Sanata Barau ya kuma jaddada ƙudurin gwamnatin Shugaba Tinubu na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ’yan Najeriya, tare da ci gaba da aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda.

Ya yaba wa Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya da JIBWIS bisa shirya taron, yana mai cewa zaɓar Najeriya a matsayin ƙasar da za ta karɓi bakuncin taron na nuna muhimmiyar rawar da ƙasar ke takawa wajen tattauna batutuwan tsaro da ci gaban nahiyar Afrika.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments