Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Khalifan Tijjaniyya na Ƙasa, Sheikh Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ganawar, wadda ta gudana ranar Laraba, ta mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi al’ummar Najeriya, kamar yadda aka bayyana.
A yayin ziyarar, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya miƙa wa Shugaba Tinubu takardar gayyatar halartar Maulidin Shehu Ahmad Tijjani, wanda aka shirya gudanarwa ranar Lahadi mai zuwa a Jihar Kano.