Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya bukaci ’yan Najeriya su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da tawagar yaɗa labaran Sarkin Musulmi ta fitar, ta bayyana cewa rahoton ba shi da tushe, tare da jaddada cewa Mai Alfarma, a matsayinsa na jagoran addini kuma uba ga dukkan ‘yan Najeriya, ba ya goyon bayan wani ɗan takara ko jam’iyyar siyasa.
Sanarwar ta ce kofofin Masarautar Sokoto a buɗe suke ga kowa ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko akida ba, kuma Sarkin Musulmi na ci gaba da ba shugabanni da ‘yan siyasa shawara da addu’a domin zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Haka kuma, ta yi kira ga jama’a, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta da ’yan jarida, da su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa ko yaɗa su, domin kauce wa yaɗa labaran ƙarya da ka iya jawo rudani ko kuma jefa cibiyoyin gargajiya da addini cikin rikicin siyasa.