Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya musanta ikirarin cewa sabuwar waƙarsa na nufin Sheikh Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
A wata hira da ya yi da RFI Hausa, Rarara ya bayyana cewa mutane ne kawai suka ɗauka cewa waƙar ta shafi Pantami, amma a cewarsa bai ambaci sunansa a cikin waƙar ba.
Ya ce fassarar da ake yi wa waƙar ra’ayin mutane ne, ba abin da shi ya faɗa kai tsaye ba.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da waƙar ta jawo ce-ce-ku-ce da muhawara a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin an yi zambo ga tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Pantami.