Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani daga Litinin, 10 ga Agustan 2026, idan har gwamnatin tarayya ba ta biya musu buƙatunsu ba.
Ƙungiyar ta bayyana cewa tana neman inganta walwalar ma’aikata, kyautata yanayin aiki, da biyan basussukan da gwamnati ke binsu, tana mai cewa waɗannan buƙatu na da muhimmanci wajen inganta harkokin kiwon lafiya a ƙasar.
A cewar ƙungiyar, rashin ɗaukar mataki kan waɗannan matsaloli na iya yin tasiri ga ayyukan asibitoci da kuma kula da marasa lafiya a faɗin Najeriya.