Sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yi Allah wadai da kalaman Sanatan Amurka Ted Cruz kan halin tsaro a Najeriya.
Kawu Sumaila ya bayyana cewa irin waɗannan kalamai na iya haddasa rashin zaman lafiya, ƙara rura wutar rikici, tare da jefa rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya cikin haɗari.
Ya buƙaci shugabanni da masu ruwa da tsaki su kasance masu yin kalamai wanda za su wanzar da zaman lafiya, maimakon waɗanda ka iya ƙara tada hankalin al’umma.
Sanatan ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai da goyon bayan ƙoƙarin da ake yi wajen inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.