Majalisar Zartarwa ta Jihar Adamawa ta amince da kwangilolin da darajarsu ta kai Naira biliyan 2.75, domin gina gidaje na dindindin ga iyalan da rikici ya raba da muhallansu a ƙaramar hukumar Madagali. Haka kuma, ta amince da inganta tsaro a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Fufore.
An amince da ayyukan ne a taron Majalisar Zartarwa karo na 11 na shekarar 2026, wanda Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya jagoranta a Fadar Gwamnati da ke Yola. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabaru, James Iliya, ya ce ayyukan na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na tallafa wa waɗanda rikici ya shafa da kuma farfaɗo da yankunan da rikici ya lalata.
Majalisar ta ware Naira biliyan 1.97 domin gina gidaje 108 masu haɗe-haɗe a Madagali ƙarƙashin shirin “Return to Ancestral Home Pathway.” An ce shirin zai taimaka wa mutanen da rikici ya raba da muhallansu su koma garuruwansu tare da sake fara rayuwa.
Kwamishinan Ma’aikatar Farfaɗowa da Agajin Jin-ƙai, Bello Hamman Diram, ya ce gidajen za su samar da matsuguni na dindindin ga iyalan da har yanzu ke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira ko kuma a gidajen masu masaukinsu.
Hakazalika, majalisar ta amince da kashe Naira miliyan 781 domin gina katanga da ƙofar shiga a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Fufore. Kwamishinan Ilimi, Dr. Garba Pella, ya ce aikin zai ƙarfafa tsaron makarantar, kare ɗalibai da malamai, tare da hana shiga ba bisa ƙa’ida ba.