Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaADC ta buƙaci Tinubu ya sauya manufofin tattalin arziki ko ya sauka...

ADC ta buƙaci Tinubu ya sauya manufofin tattalin arziki ko ya sauka daga mulki

Jam’iyyar ADC ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa, tana mai cewa idan ba a sauya su ba, ya kamata ya sauka daga mulki.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, jam’iyyar ta soki abin da ta kira manufofin tattalin arziki na “neoliberal”, tana zargin cewa sun ƙara jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali da tsadar rayuwa.

ADC ta ce damuwarta ta ƙaru ne bayan rahoton Bankin Duniya, wanda ya nuna cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 139 na rayuwa cikin talauci.

Jam’iyyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin rage tsadar rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da samar da ingantattun manufofi da za su sauƙaƙa wa ’yan ƙasa rayuwa.

Sai dai gwamnatin tarayya ta sha bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da take aiwatarwa na da nufin gyara matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar, kuma za su haifar da ɗorewar ci gaba a nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments