Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiKwana 5 bayan an ba shi beli, har yanzu ba a saki...

Kwana 5 bayan an ba shi beli, har yanzu ba a saki Dr. Bashir Kurfi ba

Kwana biyar bayan wata Kotun Majistare da ke Katsina ta ba shi beli kan zargin bata suna, har yanzu jami’an ƴan sanda ba su saki masanin harkokin tsaro kuma malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Dr. Bashir Kurfi, ba. Lamarin ya haifar da damuwa daga lauyoyinsa da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam.

Lauyan Kurfi, Barrista A. D. Umar, ya ce kotun ta amince da belin tun ranar 14 ga Yuli, kuma sun cika dukkan sharuɗɗan da aka gindaya. Sai dai duk da haka, ya ce har yanzu ba a aiwatar da umarnin kotun ba.

Ya bayyana ci gaba da tsare wanda yake karewa a matsayin abin da ya saɓa wa doka, yana mai cewa hukumomin tsaro ya kamata su mutunta umarnin kotu tare da gaggauta sakin sa.

An gurfanar da Dr. Bashir Kurfi ne bisa zargin bata suna da yaɗa bayanan ƙarya bayan wasu kalamai da ya yi a wata hira da Trust TV, inda ya yi zargin cewa gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin aikin Hajji ga wasu shugabannin ƴan bindiga. Sai dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ƴan sandan Jihar Katsina ba ta bayyana dalilin da ya sa ba a saki Dr. Bashir Kurfi ba duk da umarnin kotu da kuma cika sharuɗɗan belin da aka ba shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments