Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen wayar da kan jama’a domin rage yaɗuwar cutar sikila a jihar Kano.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai da aka shirya domin bikin Ranar Cutar Sikila ta Duniya ta shekarar 2026.
Taron ya haɗa limaman Musulunci da na Kiristanci, kuma an gudanar da shi ne ƙarƙashin taken “Wayar da kai ta hanyar addinai kan rigakafin cutar sikila da gwajin jini a jihar Kano.”
Taron ya tattauna rawar da cibiyoyin addinai za su taka wajen rage yawaitar cutar ta hanyar wayar da kai, ba da shawara kafin aure da kuma gwajin jini.
Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Kano, wanda Fasto Bitrus Nuhu ya wakilta, ya bayyana cewa cutar sikila wata mummunar cuta ce da ake gada, wadda ke jefa iyalai da al’umma cikin matsaloli.
Ya buƙaci masu shirin aure su rika yin gwajin jininsu kafin aure, tare da kira ga gwamnati da ta samar da magani mai rahusa ga masu fama da cutar tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙungiyoyin lafiya.
Shi ma Shugaban Majalisar Malamai ta Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya jaddada muhimmancin wajabta gwajin lafiya kafin aure.
Ya ce ya kamata a tilasta masu shirin aure su gabatar da shaidar gwajin HIV, jini (genotype), cutar hanta da sauran muhimman gwaje-gwajen lafiya kafin a ɗaura musu aure.
Babbar Darakta kuma Shugabar Sickle Cell Foundation Nigeria, Dakta Annette Akinsete, ta ce Najeriya ce ke da mafi yawan masu fama da cutar sikila a duniya.
Ta bayyana cewa cutar ana gadonta ne kuma tana shafar haemoglobin, sinadarin da ke ɗaukar iskar oxygen a cikin jajayen ƙwayoyin jini.
A cewarta, “Najeriya ce ke ɗauke da mafi girman nauyin cutar sikila a duniya,” inda ta ƙara da cewa cutar na jefa iyalai cikin damuwa ta fuskar tunani da kuma kuɗaɗen jinya.
Ta kuma buƙaci limaman addinai su sanya gwajin jinsin jini ya zama sharadi kafin a ɗaura aure a coci ko masallaci.