Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiDattawan da aka sace yayin zaman sulhi sun kuɓuta bayan biyan Naira...

Dattawan da aka sace yayin zaman sulhi sun kuɓuta bayan biyan Naira miliyan 35 a Zamfara

Dattawan da aka yi garkuwa da su yayin da suka je zaman sasanci da ’yan bindiga a yankin Magamin Diddi da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara sun kuɓuta bayan an biya kuɗin fansa da ya kai kimanin Naira miliyan 35.

Majiyoyi sun ce mutum uku daga cikin dattawan da aka sace sun rasa rayukansu a hannun masu garkuwa da su kafin a saki sauran bayan sun shafe sama da makonni uku a tsare.

An yi garkuwa da dattawan ne a farkon watan Yunin 2026, lokacin da suka kafa kwamiti domin tattaunawa da masu garkuwa da mutane da nufin samar da zaman lafiya a yankin.

Sai dai da isarsu wurin tattaunawar, ’yan bindigar suka kama su tare da kai su maboyarsu.

Bayan kwanaki da dama ana tattaunawa, an samu sakin waɗanda suka tsira ne bayan biyan kuɗin fansar da aka kiyasta ya kai Naira miliyan 35.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments