Sakataren Baitul Malin Amurka, Scott Besant, ya bayyana cewa China ce kaɗai ƙasar da ke ci gaba da sayen man Iran, yayin da yawancin ƙasashe suka daina saboda tsoron sake kakaba takunkuman Amurka.
A cewarsa, bayan cimma wata yarjejeniya tsakanin Washington da Tehran, Amurka ta dakatar da wasu takunkuman da suka shafi man Iran na tsawon kwanaki 60.
Duk da haka, ya ce mafi yawan ƙasashe ba su koma sayen man Iran ba.
Besant ya ƙara da cewa ci gaba da dogaro da China kaɗai wajen fitar da mai ya sa Iran ke sayar da man nata a farashi mai rahusa, kuma hakan na ƙara matsa mata lamba wajen neman kyautata dangantaka da Amurka.