Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZa a garkame Tehran ranar Talata saboda jana’izar Ayatollah Khamenei

Za a garkame Tehran ranar Talata saboda jana’izar Ayatollah Khamenei

Gwamnatin Iran ta sanar da cewa za ta rufe babban birnin ƙasar, Tehran, a ranar Talata 7 ga watan Yuli, domin sauƙaƙa gudanar da jana’izar marigayi Jagoran Koli na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Mai magana da yawun gwamnatin Iran, Fatemeh Mohajerani, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin rage cunkoson ababen hawa tare da bai wa dubban masu makoki damar halartar jana’izar cikin sauƙi da kuma komawa gidajensu ba tare da wata matsala ba.

Ta kuma sanar da cewa gwamnatin ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar zaman makoki a faɗin ƙasar domin girmama marigayin.

Ana sa ran za a binne Ayatollah Ali Khamenei a birnin Mashhad ranar Alhamis 9 ga watan Yuli, bayan kammala jerin bukukuwan jana’iza da aka tsara gudanarwa a biranen Tehran, Qom da Mashhad daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Yuli.

Baya ga Iran, an kuma shirya gudanar da bukukuwan tunawa da marigayin a wasu muhimman biranen ƙasar Iraq, da suka haɗa da Bagadaza, Kazmain, Karbala da Najaf, inda mabiyansa da sauran al’ummar Musulmi za su gudanar da addu’o’i da tarukan girmamawa.

Ayatollah Ali Khamenei ya rasu ne bayan hare-haren sama da aka kai a Iran, lamarin da ya janyo martani daga ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban a faɗin duniya, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen yi masa bankwana ta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments