Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAn fara zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu bayan cikar wa’adi

An fara zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu bayan cikar wa’adi

An fara zanga-zangar ƙyamar baƙi a sassa daban-daban na Afirka ta Kudu bayan cikar wa’adin da wasu ƙungiyoyi suka bai wa baƙin da ba su da takardun zama su fice daga ƙasar.

Lamarin ya sa hukumomi suka jibge jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci saboda fargabar barkewar rikice-rikice, yayin da Shugaba Cyril Ramaphosa ya buƙaci masu zanga-zangar su guji tashin hankali tare da gudanar da zanga-zangarsu cikin lumana.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun fara tserewa daga yankunan da abin ya shafa saboda tsoron hare-hare, yayin da hukumomi suka bayyana cewa tuni an mayar da sama da mutum 25,000 kasashensu, yawancinsu daga wasu ƙasashen Afirka.

A birnin Johannesburg, inda ake gudanar da wasu daga cikin zanga-zangar, an samu tsaiko a harkokin yau da kullum, inda shaguna da dama suka rufe saboda fargabar tashin hankali, yayin da dubban baƙi ke ci gaba da jiran a kwashe su daga sansanonin wucin gadi domin tsira da lafiyarsu.

A nasa ɓangaren, Shugaba Ramaphosa ya jaddada cewa baƙin da ke zaune a ƙasar bisa doka suna da haƙƙi kamar sauran ’yan ƙasa, yana mai cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin Afirka ta Kudu.

A birnin Durban kuwa, ana ci gaba da rushe sansanonin da ke ɗauke da ’yan Malawi, yayin da wasu daga cikinsu ke bayyana takaicinsu na barin iyalansu da rayuwar da suka fara ginawa sakamakon matsin lamba da matsalar tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments