Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da yaƙi da fataucin ƙwayoyi da kuma masu ta’ammali da su a faɗin Najeriya.
Tinubu ya bayyana hakan ne jiya a Abuja yayin bikin rufe ayyukan tunawa da Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Ƙwayoyi ta Duniya, wanda Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta shirya. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ne ya wakilce shi a wajen taron.
Shugaban ya ce gwamnati na ƙoƙarin samar da kyakkyawan yanayi da zai bai wa matasa damar rayuwa mai amfani, yana mai cewa wannan ne ya sa ake ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai wajen yaƙar shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ya kuma yabawa jami’an NDLEA bisa ƙoƙarinsu na kama dillalan ƙwayoyi da kuma hana safarar miyagun ƙwayoyi a cikin gida da wajen Najeriya.
A nasa jawabin, Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya, ya bayyana cewa hukumar ta kama miyagun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram miliyan 5.3, waɗanda darajarsu ta kai naira tiriliyan 1.5, a cikin watanni 18 da suka gabata.