Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiJihar Kano ce kan gaba a Najeriya wajen Sabbin masu rajistar katin...

Jihar Kano ce kan gaba a Najeriya wajen Sabbin masu rajistar katin zaɓe

Jihar Kano ta zama jiha mafi yawan sabbin masu rajistar katin zaɓe a Najeriya, inda mutum 441,845 suka yi rajista zuwa ranar 15 ga Yunin 2026 a ƙarƙashin shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe, CVR.

Jihar Kano ta zama jiha mafi yawan sabbin masu rajistar katin zaɓe a Najeriya, inda mutum 441,845 suka yi rajista zuwa ranar 15 ga Yunin 2026 a ƙarƙashin shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe, CVR.

Rahoton wani kwamitin gwamnatin jihar ya nuna cewa wannan nasara ta samo asali ne daga yaƙin neman rajista da shirye-shiryen wayar da kan jama’a da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gudanar, musamman domin ƙarfafa matasa su shiga harkokin zaɓe.

A cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar, Bichi ce ta fi yawan sabbin masu rajista da mutum 30,806, sai Kumbotso mai 18,701, Nasarawa mai 18,184, da Dawakin Tofa mai 17,748.

Rahoton ya kuma bayyana cewa yankunan birane da kewaye sun fi samun yawan masu rajista, yayin da aka ba da shawarar ƙara wayar da kan jama’a a ƙananan hukumomin da adadin rajistar ya yi ƙasa tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da INEC domin ci gaba da aikin rajistar.

SourcePunch
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments