Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTallafin abinci ba mafita ba ce ga iyayen waɗanda aka sace –...

Tallafin abinci ba mafita ba ce ga iyayen waɗanda aka sace – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sace ɗalibai da malamansu a Jihar Oyo, yana mai bayyana lamarin a matsayin wata alama ta yadda matsalar tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba, Atiku ya ce garkuwa da ɗaliban ya sake bayyana gazawar gwamnati wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar al’ummar ƙasar.

Ya bayyana damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa an kai kayan tallafi ga iyalan waɗanda aka sace, yana mai cewa irin wannan mataki ba zai rage raɗaɗi da damuwar iyayen ba muddin har yanzu ‘ya’yansu na hannun masu garkuwa da mutane.

Atiku ya jaddada cewa abin da iyalan ke buƙata a wannan lokaci shi ne a gaggauta ceto ɗaliban da malamansu tare da tabbatar da dawowarsu gida cikin ƙoshin lafiya, maimakon mayar da hankali kan rarraba kayan tallafi.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ceton waɗanda aka sace tare da ɗaukar matakan da za su hana sake aukuwar irin wannan lamari a makarantu da sauran wuraren jama’a.

A cewarsa, hare-haren masu garkuwa da mutane da sace ɗalibai na ci gaba da haifar da fargaba a tsakanin al’umma, lamarin da ke buƙatar matakan gaggawa da za su dawo da tsaro da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments