Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana aiki kan tsare-tsare daban-daban domin faɗaɗa damar da jama’a za su samu wajen mallakar gidaje masu kyau da araha.
Kwamishinan bunkasa gidaje na jihar Kano, Arc. Ibrahim Yakubu Adamu, ya bayyana hakan a taron Renewed Hope Housing PPP Summit 2.0 da aka gudanar a dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua Abuja.
Ya ce gwamnati na mai da hankali wajen inganta samar da gidaje ta hanyar sauƙaƙa hanyoyin da masu nema za su bi domin samun damar amfana.
Sanarwar dai an sa hannu ne da Adamu Abdullahi, Daraktan Wayar da Kai, a ranar Talata.
A cewarsa, jihar Kano na amfani da tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP) domin sauƙaƙa samun gidaje ga ‘yan ƙasa. Ya kuma yaba wa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya wajen inganta rayuwar jama’a da kuma magance ƙarancin gidaje a Najeriya.
Da yake magana kan taken taron mai cewa “From Policy To Projects Financing and Delivering Housing at Scale Through PPPs,” Kwamishinan ya ce ya dace da abin da Kano ke aiwatarwa a yanzu. Ya ƙara da cewa jihar ta riga ta karɓi shawarwarin ayyuka daga ƙwararrun abokan hulɗa, kuma ana ci gaba da duba su.
” An karɓi shawarwari, kuma nan ba da jimawa ba za a yi nazari a kansu domin tabbatar da ganin an cimma manufar samar da gidaje don amfanin al’umma,” in ji Kwamishinan.
Ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da gina rukunin gidaje 480 a ƙarƙashin aikin Gida-Gida Mega City a Rijiyar Gwan-Gwan, kan hanyar Maiduguri.
Aikin zai ƙunshi kayayyakin more rayuwa na zamani da suka dace da birni na zamani.