Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu nasarar sulhunta wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC biyu a yankin Kano ta Arewa, domin ƙarfafa haɗin kai gabanin zaɓe mai zuwa.
A wani babban taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano a daren Talata, gwamnan ya sasanta tsakanin tsohon ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.
Daraktan yaɗa labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya tabbatar da sulhun cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce taron ya ƙare ne da Gwarzo ya sanar da janye takararsa ta sanata domin mara wa Sanata Barau Jibrin baya.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai, Abubakar Kabir Bichi, da shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa da sauransu.
Ana kallon wannan mataki a matsayin babbar nasara wajen ƙarfafa APC a yankin sanatan Kano ta Arewa, inda rikicin cikin gida ya fara barazana ga haɗin kan jam’iyyar.
Bayan janyewar tasa, Gwarzo ya bayyana biyayyarsa ga muradun jam’iyyar tare da nuna shirinsa na yin aiki tare da Barau a zaɓe mai zuwa.