Akalla manoma biyu da shanu 21 aka kashe a wasu hare-hare daban-daban da suka faru a ƙananan hukumomin Riyom da Jos ta Kudu na Jihar Plateau ranar Lahadi.
Hari na farko ya faru a yankin Gero da ke Jos ta Kudu, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan makiyaya tare da jikkata mutum ɗaya da kashe shanu 21.
Hari na biyu kuma ya auku a ƙauyen Kyeng da ke Riyom, inda aka yi wa wasu matasa biyu kwanton bauna tare da kashe su. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Peter Dung mai shekaru 22 da Amos Bele Danbwarang mai shekaru 19.
Ƙungiyar Berom Youth Moulders Association, BYM ta yi Allah wadai da harin tare da kira ga jami’an tsaro su kamo masu hannu a lamarin.
Haka kuma shugaban Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, reshen jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da harin kan makiyayan tare da buƙatar ƙarin matakan tsaro domin hana sake faruwar irin hakan.
Rahotanni sun ce an tura jami’an tsaro zuwa yankunan yayin da ake ci gaba da fama da matsalolin tsaro a wasu sassan jihar Plateau.