Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeMinistan harkokin wajen Iran ya gana da takwaransa na ƙasar China a...

Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwaransa na ƙasar China a birnin Beijing

Iran da China sun gudanar da ganawar diflomasiyya yayin da ministocin harkokin waje na ƙasashen biyu suka haɗu a Beijing.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi wata ganawa da takwaransa na kasar China Wang Yi a birnin Beijing.

China wadda babbar kawar Iran ce tana yin biris da takunkuman da Amurka ta kakaba, ta hanyar ci gaba da shigo da danyen mai daga Iran zuwa matatunta.

Tafiyar Mista Araghchi na zuwa ne gabanin ziyarar da shugaba Trump zai kai China a mako mai zuwa, inda zai gana da shugaba Xi Jinping.

Mista Trump ya jinkirta ziyarar tasa ne bayan da gwamnatinsa da Isra’ila suka kai wa Iran hari a karshen watan Fabrairu.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments