Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZa a hukunta masu hannu a badakalar kuɗin ma’aikata Naira biliyan 1.5–...

Za a hukunta masu hannu a badakalar kuɗin ma’aikata Naira biliyan 1.5– Gwamnan Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta binciki batun yanke albashin ma’aikatan jihar Kano.

Ya bayyana haka ne bayan da shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Kano, Kabiru Inuwa, ya koka kan kalaman da kwamishinan yaɗa labarai Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi.

A kalaman nasa, Waiya ya zargi tsohon Shugaban ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa, da almundahanar kuɗi har Naira biliyan 1.5.

A martaninsa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a hukunta duk wanda aka kama yana da hannu a cikin badakalar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments