Hukumar JAMB ta karyata wani sakamakon jarabawar UTME da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna cewa wata ɗaliba daga Cross River State ta samu maki 394 a jarrabawar bana ta 2026.
An wallafa sakamakon a dandalin X na wani mai amfani da ake kira @Onsogbu, inda aka nuna cewa wata ɗaliba mai suna Okon Winniefred Sampson ta samu maki 96 a Turanci, 99 a Biology, 98 a Chemistry, da 99 a Physics.
Da yake mayar da martani, kakakin JAMB, Fabian Benjamin, ya ce wannan sakamakon ƙirƙirarre ne kuma bai fito daga hukumar ba.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Benjamin ya bayyana cewa a halin yanzu ana takaita sakamakon UTME ne ga tsarin dubawa kawai, kuma ba a tsara shi domin a buga ko a rarraba shi kamar yadda aka gani a wannan takarda ba.
Ya kuma ƙara da cewa tsarin da aka tsara sakamakon da yadda aka gabatar da shi ba su yi daidai da sahihin tsarin JAMB ba. Haka kuma, lambar rajista da aka nuna a takardar ba ta yi daidai da tsarin lambobin da hukumar ke samarwa ba.
A cewarsa, akwai kura-kurai da dama a cikin takardar da ke nuna cewa ba sahihiya ba ce.
JAMB ta shawarci jama’a da su yi watsi da wannan labari, su kuma dogara kawai da sahihan bayanai da hukumar ke fitarwa ta hanyoyin sadarwa na hukuma, tana mai jaddada cewa a halin yanzu ana iya duba sakamakon UTME ne kawai ta tsarin dubawa wato view-only.