Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMDD ta yaba wa Amurka kan tsawaita yarjejeniyar dakatar da hare-hare tsakaninta...

MDD ta yaba wa Amurka kan tsawaita yarjejeniyar dakatar da hare-hare tsakaninta da Iran

MDD ta ce tsawaita dakatar da buɗe wuta da Amurka ta yi abu ne mai kyau da ya dace a wannan lokaci.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi maraba da sanarwar da Shugaba Trump ya yi ta tsawaita dakatar da buɗe wuta da Iran har sai an kammala tattaunawa.

Mai magana da yawun Antonio Guterres, ya bayyana hakan a matsayin mataki mai alfanu, da zai bayar da damar samun maslahar diflomasiyya.

A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta Trump ya yi gargadin cewa, Amurka za ta ci gaba da toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran, har sai Iran ɗin ta gabatar da abin da ya kira matsayi na bai ɗaya a kan tattaunawar.

Duk da tsawon lokacin wannan rikici Trump na amfani da shafin sada zumunta da sanarwa a talabijin ya yi gargadi ga Iran.

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif wanda ke shiryawa da karɓar baƙucin tattaunawar ya ce yana fatan ɓangarorin biyu za su ci gaba da mutunta dakatar da buɗe wutar.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments