Wani babban kwamandan Iran, Janar Majid Mousavi, ya yi gargadi ga kasashen Labarawa kan rikicin da ke faruwa.
Majid Mousavi ya bayyana cewa masana’antun man fetur a yankin Gulf na iya cikin hadari idan rikici ya sake ɓarkewa a yankin.
Rahoton Al Jazeera ya bayyana cewa Mousavi ya yi wannan gargadi ne kai tsaye ga kasashen yayin da ake ci gaba da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Duk wannan rigima dai ta biyo bayan rugujewar sulhu da aka shirya tsakanin Iran da Amurka a kasar Pakistan domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Hakan ya biyo bayan shafe kusan wata biyu ana bata kashi tsakanin Iran da Isra’ila wacce ke samun goyon bayan Amurka.
An fara kai harin ne a ranar Asabar 28 ga watan Faburairun shekarar 2026 a birnin Tehran wanda ya yi ajalin manyan jami’an tsaro.