Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn yi jana’izar Brig.-Janar Oseni Braimah tare da wasu sojoji 7 da...

An yi jana’izar Brig.-Janar Oseni Braimah tare da wasu sojoji 7 da suka rasu a harin ƴan ta’adda

An gudanar da jana’izar Brig.-Janar Oseni Braimah tare da shauran sojoji bakwai da suka rasu a harin ta’addanci a jihar Borno, inda aka binne su da cikakkiyar girmamawar soja a Maiduguri.

An gudanar da jana’izar Brig.-Janar Oseni Braimah tare da shauran sojoji bakwai da suka rasu a harin ta’addanci a jihar Borno, inda aka binne su da cikakkiyar girmamawar soja a Maiduguri.

Jana’izar ta samu halartar manyan jami’an soja, gwamnati da kuma iyalan mamatan, cikin yanayi mai cike da alhini da jimami.

Sojojin sun rasa rayukansu ne yayin da suke bakin aiki bayan wani hari da ’yan ta’adda suka kai kan sansanin soja a yankin Benisheikh na ƙaramar hukumar Kaga.

Rahotanni sun nuna cewa sun mutu ne a ƙoƙarin su na kare ƙasa da al’ummarta daga barazanar tsaro.

A yayin jana’izar, an bayyana su a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayuwarsu domin tsaron Najeriya. An kuma jaddada cewa gudunmawar su ba za ta taɓa shafewa baba, tare da alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar tsaro da kuma kula da iyalan waɗanda suka rasu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments