Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMatsayarmu na nan, babu sulhu da ‘yan bindiga – Gwamna Dauda Lawal

Matsayarmu na nan, babu sulhu da ‘yan bindiga – Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da tsauraran matakai, yana cewa babu sulhu da ‘yan bindiga.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ‘yan bindiga ba, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da daukar tsauraran matakai domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Kamar yadda Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Mahmud Mohammad Dantawasa, ya bayyana a cikin wata sanarwa, matsalar tsaro na ci gaba da kawo cikas ga rayuwar al’umma, tare da hana bunkasar tattalin arziki da kuma jefa jama’a cikin fargaba.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce tana ci gaba da daukar matakan da suka hada da dabarun tsaro da kuma hada kai da masu ruwa da tsaki domin magance matsalar gaba daya.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments