Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya goyi bayan yajin aikin gama gari da kungiyar likitoci masu neman kwarewa, NARD ta sanar, kan shirin gwamnatin tarayya na dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus.
Sakataren NARD, Shuaibu Ibrahim, ya bayyana cewa za a fara yajin aikin daga karfe 12 na dare ranar Talata, 7 ga Afrilu, bayan gwamnati ta yi yunkurin dakatar da yarjejeniyar da aka riga aka cimma da likitocin.
A martaninsa, Atiku ya ce bai kamata likitoci su rika rokon abin da aka riga aka amince da shi ba, yana mai bayyana matakin gwamnati a matsayin “cin amana”.
Ya ce likitocin su ne ginshikin tsarin asibitocin da ke cikin mawuyacin hali, suna aiki a yanayi mai wahala tare da albashi mara gamsarwa, sannan yanzu ana kokarin kwace abin da aka yi musu alkawari.
Atiku ya bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta biya bashin alawus na watanni 19, da sauran hakkokin da ake binsu, yana gargadin cewa yawan likitocin da ke barin Najeriya zuwa kasashe kamar Birtaniya, Canada da Saudiyya na nuna gazawar shugabanci.
Ya kammala da cewa: “Ina tare da NARD. Ku biya abin da kuke bi, ku cika alkawarin da kuka dauka, ko ku bayyana wa ‘yan Najeriya dalilin da zai sa asibitoci su tsaya da aiki.”