Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKano da Turkiyya sun ƙarfafa haɗin gwiwa domin bunƙasa ci gaba

Kano da Turkiyya sun ƙarfafa haɗin gwiwa domin bunƙasa ci gaba

Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada ƙudirinta na ƙarfafa alaƙar aiki da ƙasar Turkiyya domin inganta ci gaban tattalin arziki da walwalar al’umma.

Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da sabon jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ya kai ziyarar aiki da gabatar da kai a fadar gwamnatin Kano.

Gwamnan, wanda Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, Dakta Sulaiman Wali ya wakilta, ya ce ziyarar jakadan ta zo a daidai lokacin da gwamnatin ke ƙoƙarin sauya fasalin tattalin arzikin jihar, da kuma inganta kyan birni da rayuwar al’umma.

Dakta Wali ya bayyana cewa jakadan ya yi alƙawarin ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa, musamman ta fuskar dawo da zirga-zirgar jiragen saman Turkiyya zuwa Kano, haɓaka harkokin noma, ilimi, da kuma tallafa wa shirye-shiryen bunƙasa ababen more rayuwa a jihar.

A nasa jawabin, jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ya jaddada aniyar ƙasarsa na ƙara ƙarfafa alaƙar kasuwanci da haɗin gwiwa da Kano, yana mai cewa akwai dimbin damammaki da za su taimaka wajen samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa ziyarar na daga cikin matakan ƙarfafa hulɗar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Turkiyya, tare da buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa a fannoni daban-daban.

Jakadan ya kuma tabbatar da cikakken goyon bayan ƙasarsa ga dukkan tsare-tsaren ci gaba da gwamnatin Kano ke aiwatarwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments