Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Juma’a da Litinin, 3 da 6 ga Afrilu, 2026, a matsayin ranakun hutun bikin Easter da Good Friday.
Wanda hakan zai sanya rufe ma’aikatu a ranakun domin samun damar yin bikin da Kiristoci ke gudanarwa duk shekara.
Rahotanni sun nuna cewa an samu bayanai kan hutun kwanaki biyu da gwamnatin Najeriya ta bayar ne a wata sanarwa da ma’aikatar cikin gida ta fitar ranar Laraba, 1 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar ta fito ne daga bakin ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, a madadin gwamnatin tarayya, inda ya mika sakon taya murna ga dukkan Kiristoci a fadin Najeriya.
Babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, wacce ta sanya hannu kan sanarwar, ta bukaci ‘yan kasa da su dauki lokacin bikin a matsayin dama don yin aiki da darasin sadaukarwa da soyayya da Yesu Kiristi ya koyar.