Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya dawo gida Najeriya bayan ziyarar aiki da ya kai Birtaniya

Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan ziyarar aiki da ya kai Birtaniya

Bayan hutu da ziyarar kasashen waje, Tinubu ya dawo Abuja don cigaba da harkokin mulki.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Abuja bayan kammala hutun Sallah karama da kuma ziyarar aiki a ƙasar Birtaniya.

Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce shugaban ya dawo Najeriya da safiyar Juma’a, inda ya halarci sallar Idi a Dodan Barracks da ke Legas.

A lokacin zamansa a Legas, Tinubu ya gana da gwamnoni 23 ciki har da gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, da kuma attajirin Afirka, Aliko Dangote.

Haka kuma ya karɓi tawagar Tarayyar Turai da mambobin GAC na Legas.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi masa bayani kan ziyararsa zuwa Borno bayan harin kunar bakin wake.

Manyan jami’ai da shugabanni ciki har da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, be suka raka shugaban zuwa filin jirgi kafin tafiyarsa.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments