Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiSenegal ta yi karar CAF da ƙasar Morocco bisa kwace mata kofi...

Senegal ta yi karar CAF da ƙasar Morocco bisa kwace mata kofi da aka yi.

Kotun warware rikicin wasanni, wato Court of Arbitration for Sport, ta tabbatar da cewa ƙasar Senegal ta shigar da ƙara domin ƙalubalantar hukuncin da Hukumar kwallon Kafa ta Afirka CAF ta yanke na kwace mata kofin AFCON na 2025.

Kotun warware rikicin wasanni, wato Court of Arbitration for Sport, ta tabbatar da cewa ƙasar Senegal ta shigar da ƙara domin ƙalubalantar hukuncin da Hukumar kwallon Kafa ta Afirka CAF ta yanke na kwace mata kofin AFCON na 2025.

Kotun da ke Lausanne ta bayyana cewa ta karɓi ƙarar daga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) a ranar Laraba.

A baya ne dai, kasar Senegal ta lashe gasar AFCON ta 2025 da ci 1-0 bayan ƙarin lokaci, duk da cewa ‘yan wasan sun fice daga fili na mintuna 15 suna zanga-zanga kan bugun fanareti da aka bai wa Morocco, wanda ba su zura ba kafin Senegal ta ci wasan.

Sai dai Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Morocco ta shigar da ƙara ga CAF, tana buƙatar a ba ta nasara ta hanyar doka da ci 3-0, bisa wasu dokoki—kuma daga bisani CAF ta amince da hakan.

Yanzu Senegal ta kai ƙarar zuwa CAS domin a soke wannan hukunci, inda take karar Morocco tare da CAF.

Senegal na neman kotun ta soke hukuncin CAF, tare da ba ta damar samun cikakken bayani kafin ta ci gaba da gabatar da hujjojinta.

Kotun CAS ta ce za ta naɗa kwamitin alkalai na musamman domin sauraron ƙarar, amma har yanzu ba a sanya ranar fara shari’a ba.

Darakta Janar na CAS, Matthieu Reeb, ya ce kotun na da ƙwarewa da kayan aikin da za su tabbatar an yi adalci ga dukkan ɓangarori, yana mai cewa za a yi ƙoƙarin gaggauta shari’ar tare da mutunta haƙƙin kowa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments