Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu ta yi fatali da buƙatar Mataimakin Gwamnan Kano na hana Majalisa...

Kotu ta yi fatali da buƙatar Mataimakin Gwamnan Kano na hana Majalisa tsige shi

Wata Babbar Kotun Tarayya ta ƙi amincewa da buƙatar da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya shigar domin a dakatar da shirin tsige shi da Majalisar dokokin jihar Kano ta fara.

A hukuncin da ya yanke ranar 25 ga Maris, 2026, Mai Shari’a S.M. Shaibu ya bayyana cewa mataimakin gwamnan bai cika sharuddan doka da ake buƙata ba domin a ba shi irin wannan umarni na gaggawa, wanda aka nema ba tare da sauraron ɓangarorin da ake ƙara ba.

Kotun ta kuma umurci Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo da ya miƙa duk takardun shari’ar ga waɗanda ake ƙara, domin su samu damar mayar da martani yadda ya kamata.

A gefe guda kuma, Majalisar dokokin jihar Kano ta riga ta samu nata umarnin wucin gadi tun a ranar 11 ga Maris, 2026, wanda ya hana mata.

Ico

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments