Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeIran za ta shafe shekaru goma kafin ta murmure daga barnar da...

Iran za ta shafe shekaru goma kafin ta murmure daga barnar da mukai mata – Trump

Trump ya yi ikirarin cewa Iran za ta ɗauki shekaru kafin ta sake farfaɗowa bayan hare-haren da aka kai mata

Donald Trump ya yi iƙirarin cewa Iran za ta ɗauki shekaru 10 kafin ta iya murmure daga mummunar ɓarnar da suka yi mata cikin ƙasa da makwanni 3 tun bayan ƙaddamar da yaƙi kanta.

A cewar Trump babu sauran wajen da ya rage basu lalata a ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya ba, wanda ke nuna ko a yau suka janye tare da dakatar da yaƙin Iran sai ta shafe shekaru 10 ko fiye ba tare da ta dawo hayyacinta ba.

Donald Trump ya yi iƙirarin cewa sun kammala lalata duk wani sashe mai amfani a ƙasar, ta yadda hatta makamashi zai mata matuƙar wahala ta iya ci gaba da fitarwa kamar yadda ta ke fitarwa a baya.

Kalaman na Trump na zuwa ne a dai dai lokacin da ya ke tsananta kira ga ƙasashe da su mara masa baya wajen amfani da ƙarfin soji don buɗe mashigin Hormuz da Iran ta kulle.

Tuni dai ƙasashe 5 da ya nemi ɗaukinsu suka noƙe daga wannan kira na Trump, kodayake a safiyar yau Litinin ya buƙaci ƙungiyar tsaro ta NATO da ta yi abin da ya dace wajen tabbatar da buɗe mashigin na Hormuz.

Trump wanda ya ɗora alhakin tsadar makamashi da ƙarancinsa da duniya ke gani kan Iran, ya ce da zarar aka haɗa ƙarfi wajen buɗe mashigin na Hormuz hada-hadar makamashi za ta dawo yadda ta ke kuma farashin zai sauka matuƙa.

A cewar Donald Trump Iran da kanta za ta nemi a dakatar da yaƙin saboda galabaitar da ta yi.

Sai dai kalaman na Trump na zuwa a dai dai lokacin da mahukuntan na Iran ke cewa ba zasu dakata da yaƙin ba har sai sun cimma muradansu.

Tun kafin yanzu Iran ta nanata cewa a shirye ta ke a shafe shekara guda ana gwabza yaƙin domin ta shirya dukkanin abubuwan da ta ke buƙata.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments