Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAn rufe ma’aikatar shari’a a Kano sakamakon yajin aikin lauyoyin gwamnati

An rufe ma’aikatar shari’a a Kano sakamakon yajin aikin lauyoyin gwamnati

Lauyoyin gwamnati a Kano sun dakatar da aiki tare da rufe ma’aikatar shari’a.

Lauyoyin gwamnatin Kano da ke aiki a Ma’aikatar Shari’a sun fara yajin aikin sai baba ta gani, inda suka kulle kofar shiga ma’aikatar ba tare da barin kowanne ma’aikaci shiga ma’aikatar ba.

Matakin tafiya yajin aikin dai ya biyo bayan sanarwar da shugaban kungiyar, Barrister Abdullahi Aminu Shamsu ya yi a jiya inda ya ce lauyoyin na cikin wani mawuyacin hali na rashin haƙƙiƙinsu na aiki da alawus alawus ɗinsu, da doka tace a basu.

Ya ce sun yi zama har sau biyu da gwamnatin amma shiru, don haka suka ɗauki matakin tafiya yajin aikin da babu ranar dawowarsa har sai an biya haƙƙoƙin nasu.

Ya zuwa yanzu dai lauyoyin sun ce ma’aikatar za ta cigaba da kasancewa a rufe har zuwa abun da hali zai yi.

Tun a daren jiya, kwamishinan shari’ar na Kano, Abdulkarim Kabiru Maude SAN, ya ce sun tattaunawa da shugabancin kungiyar lauyoyin.

Sai dai da alama tattaunawar ba ta haifar da komai ba.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments