Ƙasashen duniya sun fara mayar da martani kan naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addini na Iran, duk da cewa Donald Trump na Amurka yaƙi cewa komai yayin tambayar da manema labarai suka yi mishi kan naɗin duk da mara bayan da ya yi ga Isra’ila wajen shan alwashin kashe duk wanda aka naɗa a matsayin sabon jagoran.
Tun gabanin naɗin na Mojtaba Khamne’i, Donald Trump ya bayyana cewa yana son a bashi damar zaɓen wanda zai karɓi jagorancin addinin na Iran, akasin haka kuwa lamari ne da Amurka ba zata lamunta ba.
A gefe guda kuma Isra’ila ta ce yana daga cikin burin ta kashe sabon jagoran addinin na Iran.
Sai dai China a martanin da ta mayar kan naɗin na Mojtaba ta ce Iran da al’ummar Iran ke da ta cewa a abin da ya shafi naɗin jagoran addinin domin lamari ne da ya shafi tafiyarwar cikin gida babu buƙatar sa bakin ƙasashen duniya.
Ministan harkokin wajen China Wang Yi ya buƙaci ƙasashe su mutunta Iran a matsayin ƙasa ta hanyar kaucewa yiwa lamurranta na cikin gida katsalandan.
A cikin gida jam’iyyar Badr Organisation ta mabiya shi’a da ke riƙe da makamai ta yaba da naɗin na Mojtaba wanda ta ce manuniya ce kan cewa ƙasar za ta ci gaba da ɗorewa kan juyin-juya halin addinin Islama.
Haka zalika rundunar dakarun tabbatar da juyin-juya hali na ƙasar IRGC ta yi maraba da naɗin yayin da Sadiq Larijani da ke jagorancin hukumar ƙolin tafiyar da lamurran ƙasar ya bayyana Mojtaba a matsayin wanda ya cancanci muƙamin.
A gefe guda tsagin ƙungiyoyi da dama galibi waɗanda ke biyayya ga gwamnatin ta Iran an Iraqi sun fara miƙa saƙon taya murna tare da maraba da zuwa Mojtaba a matsayin sabon jagoran addinin na Tehran.