Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki firaiministan Birtaniya, Keir Starmer, kan abin da ya kira rashin taimaka wa Amurka a hare-haren da ta kai kan Iran.
A wata hira ta wayar tarho da jaridar The Sun, Trump ya ce Starmer “bai taimaka ba.
Ban taba tunanin zan ga hakan daga Birtaniya ba.”
Ya kara da cewa wannan abin takaici ne ganin dangantakar ƙasashen biyu.
A ranar Litinin, Starmer ya shaida wa majalisar dokokin Birtaniya cewa gwamnatinsa “ba ta goyon bayan sauya mulki ta hanyar hare-hare ba.”
Da farko dai Birtaniya ba ta amince Amurka ta yi amfani da sansanoninta wajen kai hari kan Iran ba, amma daga baya ta buɗe sansanonin nata domin abin da ta kira hare-haren kariya kan wasu wurare a Iran.
Trump ya kuma ce Faransa ta nuna goyon baya sosai, yana mai cewa, “Faransa ta yi abin kirki.
Amma Birtaniya ta bambanta da sauran.”