Mahukuntan Najeriya sun buɗe iyakokinsu da ƙasashen Nijar da Benin ta jihar Kebbi a jiya Litinin, kwana guda bayan wani taro tsakanin wakilcin ƙasashen a Abuja cike da fatan daidaita shige da ficen kayaki tsakanin ƙasashen.
Bayanai sun ce jami’an hukumar kwastam da ke kula da iyakokin Kamba da Tsamiya a ƙananan hukumomin Dandi da Bagudo dukkaninsu a jihar ta Kebbi sun buɗe iyakokin tare da bayar da damar zirga-zirga tsakanin ƙasashen 3.
Kafin yanzu dai mahukuntan Najeriya sun kulle iyakokin biyu sakamakon ta’azzarar matsalolin tsaro da ke barazana ga ilahirin ƙasashen 3.
Sai dai bayan mabanbantan ganawa tsakanin ɓangarorin, ƙasashen sun sahale dawowar hada-hada da nufin bunƙasa harkokinsu na kasuwanci da kuma saye da sayarwa a tsakanin al’ummominsu da galibi kan gudana ta hanyar amfani da iyakokin biyu.
Yayin buɗe iyakokin a yammacin jiya Litinin, kwanturon hukumar kwastam mai kula da yankin a jihar Kebbi Mahmud Matawalle Ibrahim ya ce bisa umarnin shugaban ƙasa ne suka buɗe iyakokin biyu don bayar da damar hada-hadar kayaki tsakanin Najeriyar da Nijar da kuma Benin.
A cewar jami’in tuni aka bayar da damar wucewa da manyan motocin dakon kayan da a baya ke tsaye akan iyakokin biyu waɗanda tuni suka shiga jamhuriyyar ta Nijar ta iyakar Tunga Jado daga iyakar Kamba ta jihar ta Kebbo.
Kwanturolan hukumar ta Kwastam da ke kula da iyakokin ya bayyana cewa dawowar hada-hada a iyakokin zai taimakawa al’ummomin ƙasashen 3 samun damar gudanar da kasuwanci tare da haɓaka tattalin arziƙi.