Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMustapha Rabi’u Kwankwaso Kwamshinan wasanni a ajiye mukaminsa

Mustapha Rabi’u Kwankwaso Kwamshinan wasanni a ajiye mukaminsa

Kwamishinan wasanni Mustapha Rabi’u ya ajiye aiki

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano kuma ɗan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ajiye aikinsa daga mukamin kwamishina.

Mustapha ya sanar da murabus ɗinsa ne ta wata sanarwa da ya wallafa, inda ya ce ya ɗauki matakin ne bayan yin dogon nazari

Ya gode wa gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa damar da ya ba shi na yi wa al’umma hidima, tare da yabawa yan majalisar zartarwa da ma’aikatan ma’aikatarsa bisa goyon baya da haɗin kai a lokacin da yake kan mukamin.

Murabus ɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauyen siyasa a jihar Kano, biyo bayan sauya sheƙar gwamnan jihar daga NNPP zuwa APC.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments