Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, OHCHR, ta bayyana karuwar amfani da hukuncin kisa a 2025 a matsayin abin da ke tayar da hankali.
Majalisar Dinkin Duniya ta dade tana kira da a soke hukuncin kisa a duk fadin duniya, tana mai jaddada cewa ‘yancin rayuwa hakki ne na asali da ya kamata a kare.
Rahotanni sun bayyana cewa karkashin yarjejeniyar kasa da kasa kan ‘yancin dan Adam, an tanadi cewa kasashen da ba su soke hukuncin kisa ba, su yi amfani da shi kawai a lokuta na musamman kan manyan laifuffuka mafi muni.
A cewar OHCHR, karuwar hukuncin kisa a 2025 ta samo asali ne daga hukunta masu safarar miyagun kwayoyi da kuma aiwatar da hukuncin kan abubuwan da ba su kai matsayin “manyan laifuffuka” ba.
Babban kwamishinan kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya ce hukuncin kisa ba ya hana aikata laifi yadda ya kamata.